Batun yawan kuɗaɗen da ƴan majalisar tarayya ke karɓa na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya, inda wani ɗanmajalisar dattawa ya bayyana yawan kuɗaɗen da yake samu na albashi da na gudanarwa duk wata a matsayinsa na sanata.
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ne ya sake bijiro da batun yawan albashin ƴanmajalisa da aka daɗe ana cecekuce a ƙasar inda ya yi zargin cewa su ke yanka wa kansu albashi mai tsoka.
A martaninsa, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila daga jihar Kano ya ce ba wasu kuɗaɗe ba ne ƴanmajalisar ke samu da har zai zama wani abin cecekuce.
Abubunwan da aka tattauna tsakanin Tinubu Buhari Jonathan da gwamnonin Nigeria
“Kuɗin da ake karɓa na albashi a wata bai kai naira miliyan ɗaya ba, idan an yi yanke-yanke yakan dawo kamar naira dubu ɗari shida da ɗan wani abu a matsayin albashi,” in ji sanatan.
Ya ce hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya ce ta yanka wa ƴanmajalisar albashin.
Sai dai Sanata Kawu Sumaila na jam’iyyar hamayya ta NNPP ya ce kudaden gudanarwa da yake samu a matsayinsa na ɗanmajalisar dattawa da ya ƙunshi har da tafiyar da ofis ya kai naira miliyan ashirin ɗaya a kowane wata.
“Saboda ƙari da aka samu, a majalisar dattawa ana ba wa kowane sanata naira miliyan ashirin da ɗaya a kowane wata a matsayin kuɗin gudanar da ofis ɗinsa,” in ji shi.
Dalilin da ya sa na fara yiwa yan siyasa bankada – Dan Bello
Ya ƙara da cewa jimillar naira miliyan 22 yake yake samu a matsayinsa na sanata.
“Ni dai ban san wani kuɗi da aka halarta ake ba ni a matsayin sanata ba,” a cewarsa.
Ya ce kuɗaɗen da yake karɓa su ne na dukkanin ayyukan da zai yi da suka haɗa da tafiye-tafiye ɗanmajalisa na cikin gida da sayen jaridu .
Sai dai ya ce bai san adadin kuɗin da shugabannin majalisar ke karɓa ba a matsayin albashi da na gudanarwa.
Sanatan ya caccaki Obasanjo inda ya ce a zamanin mulkinsa ne aka fara ba ƴanmajalisa Kudaden da suke wuce hankalin mutane da nufin gyara ga kundin tsarin mulki domin sahalewa Obasanjo yin tazarce, zargin da a baya tsohon shugaban ya musanta.
Zargin karkatar da shinkafa: EFCC ta karɓi korafi kan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano
A ranar Juma’a ne tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo wanda ya sha sukar gwamnati ya yi zargi ƴan majalisar cewa su ke yankwa kansu albashi mai tsoka da kuma hanyoyin da suke samu kuɗi fiye da ƙima.
Wannan cacar baki na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya.
Wasu ƴan ƙasar na ganin girman ɗawainiyar kula ƴanmajalisar na daga cikin dalilan da ke jefa su cikin ƙunci, wani abin da ƴanmajalisar ke ganin su aka fi saka wa ido fiye da hidimar da ake yi wa ɓangaren zartarwa.
BBC Hausa