Daga Kamal Yahaya Zakaria
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da karbar korafin da wata Kungiya ta kai mata kan zargin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano, Shehu Wada Sagagi da karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta kawo jihar.
Koken, wanda kungiyar Arewa APC Merger Group ce ta shigar da shi, wanda shugabanta na kasa Hon. Musa Mujahid Zaitawa ya sawa hannu, ya yi zargin cewa Sagagi na da hannu wajen karkatar da tallafin shinkafa na Gwamnatin Tarayya ta kawo domin raba wa ga al’ummar Jihar Kano.
Da dumi-dumi: Gwamnatin Kaduna ta janye dokar hana fita
A cewar wasikar da aka aike wa shugaban hukumar ta EFCC, kungiyar ta yi ikirarin cewa sahihan rahotanni daga kafafen yada labarai da majiya mai tushe sun nuna cewa Sagagi ya boye shinkafar ne a daya daga cikin gidansa da ke Gandun Albasa Quarters, Kano.
Wasikar ta ci gaba da cewa matasa sun kutsa cikin gidan tare da kwashe shinkafar ne yayin da ake gudanar da Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.
Dan Bello ya sanya wa jam’iyyar APCn Kano sharadin dakatar da yi mata bankade-bankade
Kungiyar ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika ta Sagagi, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin tausayi da ma da cin amanar jama’a.
Sun bukaci hukumar ta EFCC da ta yi bincike sosai kan lamarin tare da tabbatar da cewa an yi adalci, tare da jaddada amincewarsu da kudurin hukumar na tabbatar da doka da kare muradun ‘yan kasa.
Tambarin hukumar ta EFCC ya nuna cewa an karbi wasikar a hukumance a ranar 12 ga watan Agusta, 2024, wanda hakan ya tabbatar da cewa hukumar ta EFCC ta na da masaniya kan batun tunda an kai mata korafi.
Ana sa ran wannan mataki zai jawo hankulan wadanda Ke da alaka da rabon kayan tallafin da ake kawo wa don rabawa al’umma, wanda wasu ke karkatar da shi, wanda hakan yasa al’umma suke kokawa sosai.