NUJ ta Kano ta sami sabbin Shugabanni, sun yi alkawarin kare hakkin ‘yan jarida

Date:

Daga Maryam Usman

 

An rantsar da sabuwar majalisar zartarwa ta kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya NUJ reshen jihar Kano.

Sabon Shugaban ya karbi ragamar tafiyar da al’amuran kungiyar ne bayan kammala wa’adin zango biyu da tsohon shugaban Abbas Ibrahim ya yi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dantiye, ya shawarci sabbin shugabannin kungiyar da su hada kan ‘ya’yan kungiyar tare da tabbatar da ana amfani da kware wajen gudanar da aikin jarida.

Zargin karkatar da shinkafa: APC ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan jami’an gwamnatin Kano

Sabon shugaban kungiyar ta NUJ Suleiman Dederi ya yi alkawarin hada kan ya’yan kungiyar tare da ba da horo ga yan jarida da kuma tabbatar da ingantacciyar walwala yan kungiyar.

“Yayin da muke shiga wannan sabon babi, na kuduri aniyar ganin na ci gaba da bin ka’idojin aikin jarida, da yin gaskiya, da kuma fafutukar kare hakki da jin dadin dukkan ‘yan jarida a jihar Kano.”

Ya yabawa shuwagabannin NUJ da suka kammala wa’adin mulkin su bisa yadda suka hada kai da tare da Aiwatar da manufofin cigaban aikin jarida a Kano bisa kwarewa.

“Dole ne in yaba da kwazon da sadaukar da kai da suka yi yayin jagorancinsu, don haka na ke baiwa al’umma tabbacin zan dora kan aiyukan alkhairin da suka faru kuma insha Allah zan kaucewa kura-kuran da suka yi a matsayinsu na yan adam.”

A jawabinsa tsohon Shugaban NUJ reshen Kano, Abbas Ibrahim, ya bukaci sabbin shugabannin da su dauki wannan sabon nauyi da muhimmanci tare da ciyar da kungiyar ta NUJ Kano zuwa mataki na gaba.

Ibrahim ya yi godiya ga Allah da ya ba su nasara da kuma goyon bayan da suka samu daga membobin kungiyar.

Kama sojan da ya harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku

Ya lissafta nasarorin da suka samu a cikin wa’adin zango biyun da suka yi, wanda ya hadar da gina shaguna sama da 20, samar da motocin bas guda biyu, gyaran zauren NUJ da dai sauransu.

Ya bayyana rashin samun bayanai a matsayin kalubale ga masu sana’a, inda ya yi kira ga hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da su rika baiwa ‘yan jarida bayanai domin amfanin al’umma.

Taron rantsar da sabbin shugabannin reshen Kano ya samu halartar jami’an gwamnatin jihar da sauran shugabannin kungiyoyin.

Suleiman Abdullahi Dederi shi ne sabon shugaban, Mustapha Gambo Muhammad na gidan rediyon Najeriya Pyramid FM a matsayin mataimakin shugaba sai sakataren kungiyar Abubakar Kwaru da Hauwa Zaharadden mataimakiyar Sakatare sai Nura Bala Ajingi a matsayin Ma’aji, Abdullahi Hassan Sakataren kudi da kuma Jami’in bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...