Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da gurfanar da wasu mutane 632 da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati da sace kayan jama’a da yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar.

Jaridar Kadaura24 ta ruwaito cewa, an ga matasa masu zanga-zanga, suna rera wakokin nuna adawa da gwamnati da kuma rike da tutar kasar Rasha, a wurare irin su Dakata, Rimin Kebbe, Gwammja, Zoo Road da dai sauransu.
Da yake jawabi a Kano, Kakakin Gwamnan Jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa an kama wadanda ake tuhuma su 632 da laifin lalata dukiyar al’umma.
Zanga-zanga:APCn Kano ta mayar da zazzafan martani ga kalaman gwamna Abba Kabir
Dawakin Tofa ya yi gargadin cewa kudirin gwamnatin jihar Kano na wanzar da zaman lafiya ba abu ne da gwamnati zata yi wasa da shi ba, inda ya kara da cewa wadanda aka samu da laifin barna za su fuskanci doka.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar na shirin samar da dimbin shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i daban-daban domin inganta rayuwar su, domin dakile yiyuwar amfani da su wajen karya doka da oda.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya dage taron FEC, ya karbi bakuncin shugabannin tsaro
Kakakin ya kuma sanar da cewa za a kafa kwamitin bincike na musamman da zai binciki wadanda ke da hannu wajen kashe-kashe da sace-sacen kayan jama’a a jihar.
Kwamitin zai tantance musabbabin kashe-kashe da lalata gine-ginen gwamnati, in ji shi.
Ya kara da cewa masu zanga-zangar da suke dauke da tutocin kasar Rasha ba su da alaka da gwamnati, don haka ya bukaci hukumomin tsaro da su bankado wadanda ke ingiza su da kuma manufarsu.
Ya bayyana cewa masu zanga-zangar na gaskiya a jihar sun mika kokensu da bukatunsu ga gwamnati, wanda ya ce za a mika su ga shugaba Bola Tinubu.