Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaba Bola Tinubu ya dage zaman majalisar zartarwa ta tarayya na wannan makon zuwa ranar da ba a bayyana ba, kuma a maimakon haka zai gana da shugabannin hukumomin tsaro na Nigeria.
Ana sa ran taron zai samu halartar mataimakin shugaban kasa, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da dukkan hafsoshin tsaro, da sufeto janar na ‘yan sanda, da kwanturola janar na kwastam, da na hukumar kula da shige da fice, da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita
Majiyar da ke kusa da fadar shugaban kasa ta shaida wa gidan talabijin na Channels, cewa taron gaggawar da shugabannin tsaro ba zai rasa nasaba da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake yi a fadin kasar ba.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan Najeriya wadanda galibi matasa ne su ke sake haduwa domin gudanar da zanga-zangar a a fadin kasar a rana ta biyar na zanga-zangar, inda wasu daga cikinsu ke dauke da tutocin ƙasar Rasha