Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Majalisar tsaro ta jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta sanar da sanya dokar tabaci a jihar.
An sanya dokar tabacin ne bayan gagarumar zanga-zanga da ta rikide zuwa rikici a yau Litinin a garin Kaduna da Zaria.
Zanga-Zanga:Yadda Aka Yi Salloli Da Alkunut A Kano
A sanarwar da kwamishinan al’amarin cikin gida da tsaro na jihar, Samuel Aruwan ya fitar ya ce an sanya dokar ne bayan bata gari sun lalata kadarorin gwamnati da na al’umma.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro zasu ci gaba da sanya idanu don tabbatar da doka da oda a fadin jihar.