Daga Sani Idris Maiwaya, Khadija Abdullahi Aliyu, da Hamisu Isa
Duk da cewa gwamnatin jihar kano ta sanya dokar hana fita tun ranar Alhamis da aka fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Nigeria, wasu matasa na cigaba da fitowa a unguwanni daban-daban domin cigaba da gudanar da zanga-zangar.
Idan za a tunawa a ranar Alhamis ne aka fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihohin tarayyar Nigeria, sai dai a wasu jihohin zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali wanda hakan ya tilastawa hukumomi sanya dokar hana fita a jihohi kamar Kano Jigawa Katsina Yobe Nasarawa da Borno.
Rahotanni da jaridar kadaura24 ta samu tun a jiya juma’a Matasa suka rika kokarin sai sun ci gaba da yin zanga-zangar, kamar a yankin Airport Road, Bridget, Hotoro, Kurna, Rijiyar lemo da sauran wasu unguwanni dake birnin Kano.

Sai dai tun a jiyan jami’an tsaro suke ta kokarin ganin matasan ba su sake mamaye titunan birnin ba.
Haka zalika, a yau asabar ma dai rahotanni sun nuna cewa a wasu daga cikin unguwanni birnin Kano sun sake fitowa domin cigaba da yin zanga-zangar.
Wasu matasa daga yankin unguwanni kurna Rijiyar lemo sun yi ta kokarin ganin sun sake fitowa, amma jami’an tsaro suka maida su, inda daga bisani lamarin ya kazanta, Inda ake Fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu .
A wasu yankunan kuma na unguwar Kurna sallah suka yi tare da yin alkunutu da zammar Allah ya kawo wa al’umma sauƙin tsadar rayuwar da ake fama.
Da dumi-dumi: Tinubu zai yiwa yan ƙasa Jawabi
Haka ma, matasan yankin unguwanni cikin gari kamar su tal’udu, mandawari da sauransu, suma sun fito da zummar cigaba da zanga-zangar, haka suma jami’an tsaro sun yi nasarar mayar da su.
Sai dai lamarin na su ya zo da wani salo Inda suna Rika daga tutucin kasar Rasha tare da yin kira ga kasar da ta kawo musu dauki tunda America da ingila sun kasa cewa komai.
Haka lamarin ya ke dai a yankin unguwanni Bridge nan ma matasa sun fito tare da fadin cewa su zanga-zangarsu ta lumana ce , amma duk da haka jami’an tsaro ba su bar su.
A halin yanzu dai jami’an tsaro sun kara damara ta ganin al’umma sun bi dokar hana fita da aka sanya domin ganin al’amura sun koma daidai.