Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar kano ta sanar da sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya sakamakon yadda zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta rikide zuwa tashin hankali.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa gwamnatin jihar kano ta sanya dokar ne tun a ranar Alhamis ranar farko kenan da fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa bayan wasu bata gari sun fake da zanga-zangar su ka rika fasawa da sace kayan gwamnati da na al’umma.
Duk da dokar hana fita, zanga-zanga ta dau sabon salo a Kano
” Daga gobe lahadi za a fara fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana, har kuma aga abun da hali zai yi “.
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kwamshinan yaɗa labarai na jihar Kano Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu.