Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Jagoran jam’iyyar adawa a Najeriya, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da yadda jami’an tsaro a kasar suka yi amfani da harsashin mai kisa a kan masu zanga-zangar lumana.
tsohon mataimakin shugaban kasar, ya yi kira ga kasashen duniya da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da su sanya ido sosai kan lamarin.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita
“Ina yin Allah wadai da wannan danyen aikin na amfani da harsashi mai rai ga ‘yan kasar da ke zanga-zangar lumana, kamar yadda aka shaida yau a Kano da Abuja. Wannan ba abu ne da za a iya jurewa ba kuma ya tunawa mutane zamanin mulkin kama-karya na soja.
“Yana da mahimmanci a tunatar da gwamnati da hukumomin tsaro babban aikinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma kamata ya yi abar ‘yan kasa su yi zanga-zanga ba tare da tsoratarwa ba.
Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya bukaci Tinubu ya saurari koken jama’a
“Ina kira ga kasashen duniya da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da su sanya ido sosai a kan al’amuran da ke faruwa a Najeriya tare da dora alhakin abubunwan da suka faru hukumomin tsaro.
“Ina sake jaddada shawarara ga masu zanga-zangar da su jajirce wajen amfani da ‘yancinsu na gudanar da zanga-zangar lumana tare da yin watsi da duk wani tashin hankali”. A cewar Atiku
“Wadanda ke aikata satar dukiyar jama’a da lalata dukiyoyin jama’a dana gwamnati dole ne a fito da su a gurfanar da su a gaban kuliya kamar yadda doka ta tanada. Domin abun da suka yi zai iya lalata halascin zanga-zangar da doka ta bada dama a yi.
“Dole ne shugaba Tinubu ya nuna jagoranci na gaskiya ta hanyar gaggauta aiwatar da bukatun al’ummar Najeriya,” in ji Atiku Abubakar.