A ranar Litinin majalisar ministoci ta Najeriya ta bayar da umarnin a riƙa sayar da ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida a kuɗin ƙasar na naira.
A zaman majalisar na ranar Litinin da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, an buƙaci matatun man da ke ƙasar su sayar da man da aka tace a naira.
Kazalika, an umarci kamfanin mai na ƙasar NNPCL da ya tattauna da matatar man Dangote da sauran matatun mai na cikin gida da nufin kawo ƙarshen takun-sakar da ke tsakaninsu game da sayar da ɗanyen man.
Tuni dai masana suka fara tsokaci a kan gagarumin yunƙurin na daidaita farashin man fetur, da kuma farashin dala da naira da gwamnatin Najeriya ke son yi.
Sabuwar dabarar, a cewar masana, na nufin kawar da buƙatu masu sarƙaƙiya a cinikayya da ƙasashen waje da ta haɗa da musayar kuɗi, yayin da sabuwar hanyar tace man a cikin gida za ta zo da sauƙi da kuma bunƙasa tattalin arziki da masana’antu, tare da zawarcin masu zuba jari daga ƙasashen ƙetare.
Yunƙurin da Najeriya ta yi na sayar da ɗanyen mai ga Dangote a naira ya janyo hankalin ƙasashe a kasuwannin matatun man fetur da iskar gas na duniya.
Gwamnatin Kano ta musanta labarin kashe Naira Biliyan 10 wajen siyan kayan Ofis
Manazarta sun lura cewa matakin na nuna gagarumin sauyi ga manufofin makamashin Najeriya da fifita tace ɗanyen man a cikin gida maimakon fitar da shi waje a tace sannan a mayar da shi cikin gida.up
Ana sa ran matakin zai rage yawan dogaron da Najeriya ke yi kan ajiyar kuɗaɗen waje da kuma daidaita darajar kuɗin ƙasar. Kazalika, matakin zai buɗe ƙofa ga masu zuba jari.
Tinubu ya dauki matakin da zai kawo karshen dambarwar Matatar Ɗangote da gwamnatin tarayya
Alhaji Shuaibu Idris, wani mai sharhi kan al’amuran tattalin arziki a Najeriya, ya ce akwai alfanu da dama a tattare da yunƙurin na gwamnati saboda a da “sai kamfanin Dangote ya yi yawon neman dalar da zai sayi man da matatarsa za ta yi amfani da shi”.
A cewarsa, da wannan matakin na siyar wa Dangote man a naira, ba zai sha wannan wahalar ba.
“Sannan a baya sai mutum ya bi hanya mai dogon zango, amma yanzu za a samu rangwame da raguwar buƙatar dala,” in ji shi.
“Ganga 450,000 da aka ce za a sayar wa matatun mai da muke da su a ƙasar nan, da idan an siyar da gangunan man, dalar da za a karɓa, a saka ta a kasuwar hada-hadar cinikayya ko kuma hada-hadar kuɗaɗen ƙetare. Yanzu tun da za a karɓi naira ba za a samu wannan kuɗin da za a saka su a ciki ba ke nan.”
A iya cewa kamfanin Dangote ya zama zakaran gwajin-dafi, wanda za a fara sayar wa ɗanyen mai a cikin gida, yayin da sauran matatun mai na cikin gida za su bi sawu daga baya.
Masana na ganin wannan dama da matatar Dangote ta samu ta sayen ɗanyen mai babban cigaba ne.
Shu’aibu Idris ya bayyana cewa “yakamata a ce an ɗauki irin waɗannan matakai tun tuni kuma a tabbatar bai tsaya iya kamfanin Dangote ba, a sako sauran kamfanoni da ke ƙoƙarin tacewa da sarrafa sauran ma’adanai”.
Dizal dinmu na da ingancin da za a yi amfani da shi ko ina a duniya – Matatar Dangote
Al’umma a Nigeria na ganin wannan mataki zai taimaka wajen bunƙasa masana’antu, yayin da ƙasar ke tafiya cikin yanayi na rashin tabbas game da tattalin arzikinta.
BBC Hausa