Yadda Aka Kama Lakcarorin Bogi A Jami’ar Bayero dake Kano

Date:

Wasu malaman jami’a na bogi sun shiga hannun jami’an tsaro a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Dubun malaman jami’ar na bogin ta cika ne a yayin da suke tsaka da sayar wa dalibai ’yan ajin farko da litattafan karatu.

Sanarwar da jami’ar ta fitar ɗauke da sa hannun Mukaddashin Magatakarda Jami’ar BUK Bala G. Abdullahi, ta ce lakcarorin bogin sun tursasa dalibai sayen litattafansu guda hudu a matsayin sharadin cin jarabawar darussan su.

Talla
Talla

Ya ce dubun mutanen biyu, Mista David Iluebe daga Jihar Edo da Mista Chike E. Eke daga Jihar Delta, ta cika ne bayan sun shiga dakin karatu a Tsangayar Karatun Injiniya, suka gabatar da kansu a matsayin lakcarori, suka tallata musu litattafai hudu.

Lakcarorin ba su tsaya nan ba, sun bayyana wa daliban cewa sayen litattafan wajibi ne kuma babu wanda zai ci jarabawa sai wanda ya saya.

Da dumi-dumi: Tinubu ya rage farashin Shinkafa a Nigeria

Magatakardan ya ce barazanar ta tilasta wa daliban sayen litattafan, amma daga bisani take-taken lakcarorin bogin ta sa jami’an tsaron jami’ar kama su.

Bayan samun korafi aka kama su, inda a halin yanzu ake tuhumar su da laifukan kutse, sojan gona, damfara da kuma cuta.

Ya ce lakcarorin bogin sun bayyana cewa karo na biyu ke nan da suka yi haka a Kano, domin a baya sun yi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar (Kano Poly).

Sun yi ikirarin wallafa littatafan da suke sayarwa kuma sun yi haka ne saboda rashin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...