Dukiyar Abacha: Inda gwamnatin tarayya ta yi kuskure

Date:

Kafafen yada labarai sun yada labarin yadda gwamnatin tarayya karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta kwce wani fili da ke yankin Maitama a Abuja mallakin iyalan marigayi shugaban kasa, Janar Sani Abacha.

An Kwace filin ne a watan Fabrairun 2006 a lokacin da Nasir El-Rufai yake Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, bayan kuma Iyalan Abacha suna da takardar izinin mallakar filin tun a Shekarar 1993, lokacin Abacha ke rike da shugabancin kasar.

An rawaito cewa El-Rufai ya dauki matakin ne da niyyar kuntatawa Iyalan Abacha, wanda kuma ya yi hakan ne bisa umarnin mai gidansa Obasanjo.

Tsohon shugaban kasar ya bada umarnin kwace izinin mallakar filin ne da nufin cutar da iyalan Abacha. A fili yake an kwace filin ne ba don amfani jama’a ba.

Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, shi ya sake dagula lamuran, domin lokacin yana ministan Abuja, a ranar 25 ga Mayu, 2011, ya baiwa wani kamfani mai suna Salamed Ventures takardar shaidar mallakar filin, duk da cewa lamarin yana gaban kotu.

An ce Salamed Ventures Limited ya mallaki wannan fili ne a kan dala miliyan 1.3 yayin da ake ci gaba da sauraron karar a kotun daukaka kara. Tun daga wancan lokacin, iyalan Abacha da hukumomin da abin ya shafa suke ta dambarwa a gaban kotu .

Talla
Talla

A bayyane ya ke cewa an soke izinin mallakar filin daga Iyalan Abacha ne ba bisa ka’ida, domin Iyalan Abacha ba su karya dokar babban birnin tarayya ko dokar Filaye ta birnin ba yayin mallakar filin, kuma ba a yi hakan don maslahar jama’a ba, haka kuma ba wata doka da Iyalan Abacha suka karya.

Bincike ya nuna cewa babu wata hujjar shari’a da aka dogara da ita wajen soke izinin mallakar filin na iyalan Abacha.

Iyalan Abacha sun tsaya kai da fata domin su cigaba da rike filin da aka kwace musu ba bisa ka’ida ba. Mohammed Abacha da Maryam Abacha wadanda su ne masu kula da filin sun shigar da kara a gaban wata babbar kotu a watan Fabrairun 2006 karkashin Mai shari’a I.M Bukar.

Rarara ya Magantu AKan Goge Shafinsa da Facebook Ya Yi

A ranar 30 ga Yuni, 2009, Mai shari’a I.M Bukar ya yanke hukunci akan karar, inda ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren karar, kuma ya ce babbar kotun tarayyar Najeriya ce kadai take da hurumin sauraren karar.

Daga nan sai wadanda suka shigar da karar Mohammed Sani Abacha da Maryam Sani Abacha suka daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da ke Abuja a kan batun tauye musu hakkinsu.

Daga bisani, Kotun Daukaka Kara, a ranar 18 ga Mayu, 2015, ta tabbatar da hukuncin kotun ta hanyar korar karar.

Masu kara sun dauki wannan matakin na yanzu ne tun a ranar 25 ga Mayu, 2015, bisa dogaro da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Abacha ya sanar da jaridar gazettengr cewa sun mallaki filin ne tun kafin rasuwar marigayi Janar Abacha.

A farkon wannan shekarar, an shigar da karar a gaban mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya kuma a ranar 19 ga watan Yuli, 2024, ya yanke hukuncin, inda ya yi watsi da karar ta Iyalan Abachan .

Gwamnan Kano ya nada sabbin yan hukumar gudanarwar Kano Pillars, ya baiwa Ahmad Musa Mukami

Mai shari’a Lifu ya yanke hukuncin cewa iyalan Abacha ba su da hurumin da za su shigar da karar suna kalubalantar kwace musu filin da aka yi dake yankin Maitama, tare da neman a biya su diyyar Naira miliyan 500.

Sai dai kuma tuni Iyalan tsohon shugaban kasar suka shigar da kara kan hukuncin ta hannun lauyan su, Reuben Atabo (SAN), Inda ya ce kotun da ke shari’ar ta yi kuskure a kan wasu dalilai 11 na yin watsi da karar ta su.

Reuben Atabo ya sanar da manema labarai cewa za su gabatar da karin hujjoji don daukaka kara kan hukuncin.

Daukaka karar zai hadar da shugaban kasa Bola Tinubu, ministan babban birnin tarayya Abuja, hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA), da kamfanin Salamed Ventures Ltd .

Ya ce za su bukaci kotun daukakar da ta ta gingine batun sayarwa tare da mika takardar mallakar filin mai lamba 3119, dake Maitama, Abuja, mai girman hekta uku ga Salamed Ventures Ltd a ranar 25 ga Fabrairu, 2011.

A cikin karar, iyalan Abacha za su roki kotun ta yi watsi da hukuncin da Mai shari’a Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke, a ranar 19 ga watan Yuli, 2024, wanda ta yi watsi da karar da suka shigar kan filin.

Talla

Iyalan marigayin za kuma su roki kotun daukaka kara da ta yi amfani da sashe na 15 na dokar kotun daukaka kara ta karbe shari’ar da suke yi a matsayin kotun matakin farko tare da yin adalci a kan lamarin.

Amma, a cewar wani lauya mazaunin Abuja, Abdulsalam Nasiru, wadanda suka shigar da karar na da damar gabatar da karar a babbar kotun tarayya da ke Abuja kamar yadda kotun daukaka kara ta bayyana.

Malam Nasiru ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta siyar da filin yayin da batun ke gaban kotu. “Wannan matakin rashin mutunta doka ne. Matakin da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya dauka a matsayinsa na ministan babban birnin tarayya, tabbas bai yi wa ‘yan Nijeriya dadi ba.

“Matakin da aka dauka kokari ne na wulakanta iyalan tsohon shugaban kasar saboda da an ga baya raye. Sannan kuma a daya bangaren, matakin ya nuna rashin mutunta dokar amfani da filaye, wadda Iyalan Marigayin suka bi suka mallaki filin .

“Babu shakka filin da ake magana a kai, Iyalan Abacha sun neme shi tun a farkon shekararn 1990. An amince da bukata ba su fili mai lamba 3199, dake Maitama, Abuja, kuma Ministan Babban Birnin Tarayya na lokacin ne ya sa hannu akan takardar .

“Sun cika dukkanin ka’idojin da suka da ce ta hanyar mallakar duk takardu wasu takardu da suka Kamata, kafin rasuwar Abacha a ranar 8 ga Yuni 1998,” in ji shi.

Me ya sa gwamnatin tarayya ta yi kuskure?

Daga bangaren wani mai sharhi kan al’amuran al’umma Said Akintade Shittu, ya ce “Akwai wasu alamu da ke nuni da cewa tsoffin ministocin babban birnin tarayya, Nasir El-rufai da Bala Mohammed na da gillin da suke nufin iyalan Janar Sani Abachan da shi, wanda hakan ta sa gwamnatin ta yi wancan kuskuren na kwace musu filin da suka mallaka ta hanyar doka.

“Na farko, mutum na iya zargin Sani Abacha da wasu munanan ayyuka kamar sauran shugabannin da suka shude, amma babu musun cewa shi tsohon shugaban kasar nan ne. Kuma iyalansa sun mallaki filin ta halacciyar hanya.

“Na biyu, duk wanda ya shawarci El-rufai da Bala Mohammed da su sayar da filin bayan an kwace shi, duk da cewa batun filin yana gaban kotu, to shi ma ba daidai ba ne.

“Yayin da El-rufai yake tsohon gwamna, Bala Mohammed kuma shi ne gwamnan jihar Bauchi, kuma duk cikinsu babu wanda zai so a yi wa iyalansa irin wannan abun da suka yiwa Iyalan Abachan.

“Babu bukatar daukar matakin gaggawa akan batun, a bari kotu ta kammala aikinta, kafin daukar duk wani mataki kan takaddamar . Na yi imani da yawan ‘yan Najeriya suna lura da abin da ke faruwa kuma suna jiran kotun ta yi hukunci.

“Haka zalika, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta yi bincike akan batun ta kuma warware matsalar, saboda mun san shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu shugaba ne da yake mutunta doka sosai.

“Saboda haka, yana da kyau shugaban kasa ya kafa kwamitin da zai binciki rikicin filin da ya shafi iyalan Abacha da ministocin babban birnin tarayya Abuja da kuma ba da damar yin adalci. Wannan ne kadai zai iya kubutar da shi daga zargi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...