Zanga-zanga: Tinubu ya ba da umarnin tsaurara tsaro a kan iyakokin Nigeria

Date:

Gabanin zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da wasu ƴan Najeriya ke shirin yi, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin tsananta matakan tsaro a kan iyakokin ƙasar.

Shugabar hukumar shige da fice ta Najeriya, Kemi Nanna Nandap ta bayar da umarnin ga dukkan manyan jami’an hukumar masu kula shiyya, da na jihohi da kuma na ƙananan yankuna.

Kakakin hukumar shige da fice ta Najeriya, DCI Kenneth Udo a cikin wata sanarwa ya ce umarnin: “Shugabar hukumar shige da fice ta ƙasa ta umarcin dukkan kwamandojinmu a kowanne mataki, su tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro a bakin aikin su kafin zanga-zangar gama gari da wasu ƴan Najeriya ke shirin yi.’’

Talla
Talla

Ya ƙara da cewa “Shugabar hukumar ta kuma umarci kwamandojinmu masu kula da kan iyakokin Najeriya su tsaurara bincike domin hana bakin haure shiga cikin ƙasar domin aikata laifi, musamman a lokacin zanga-zangar’’.

Hukumar shige da fice ta Najeriya ta kuma hori jami’anta su gudanar da aikin su a cikin ƙwarewa da gaskiya da kuma riƙon amana, a kodayaushe.

Yanzu-yanzu: Yan Nigeria sun dauki mataki akan mawaki Rarara

Waɗanda ke barazanar zanga-zangar dai sun ce za su fita titunan Najeriya a ranar ɗaya ga watan Ogustan 2024, domin bayyana rashin jin dadin su a kan matsalar tsadar rayuwa da rashin shugabanci nagari.

Sun ƙirƙiri wani maudu’i a kafafen zada zumunta a game da zanga-zangar tasu, wanda suka kira da #EndBadGovernance.

A watan Yunin 2024, alƙalumman da hukumomi suka fitar a ƙasar sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 34.19 kuma ana alaƙata wannan tashi da janye tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi da kuma faɗuwar darajar naira.

Zanga-zangar: Yan Kasuwar Kano sun yi shirin samar da tsaro a wuraren Kasuwancinsu

Wannan ne kuma ya jefa rayuwar jama’ar ƙasar da dama cikin mawuyacin hali, ya kuma tunzura wasu domin kiran a fito domin zanga-zangar gama gari.

Talla

Tun kafin matakin da hukumar shige da fice ta Najeriya ta ɗauka, sauran hukumomin tsaron ƙasar sun yi gargaɗi game da zanga-zangar da kuma abubuwan da za su iya biyo bayan ta.

Daga cikin su akwai hukumar tsaro ta DSS wadda ta ce Manufar masu zanga-zanga ita ce “kifar da gwamnati” kuma a cikin wata sanarwa ta ce duk da cewa ta gano masu kitsa zanga-zangar da masu ba su kuɗaɗe amma hukumar tana bin hanyoyin da doka ta tanada waɗanda ba na amfani da ƙarfi ba domin daƙile zanga-zangar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...