Yadda wata dalibar jami’a ta rasu a bandaki

Date:

 

Shugabannin Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi, sun tabbatar da rasuwar Naja’atu Salisu, ɗaliba a aji uku a fannin Kimiyyar Kwamfuta.

Rahotanni sun bayyana cewar an same ta cikin mawuyacin hali a banɗaki ɗalibai bayan ta je wanka.

Daraktan yaɗa labarai na ATBU, Zailani Bappa, ya tabbatar da lamarin, ya ce an kai Naja’atu asibitin jami’ar domin ba ta agajin gaggawa, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarta.

Talla
Talla

Bappa ya bayyana cewa, “Bayan lura da hakan, an garzaya da Naja’atu zuw Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, inda likita ya tabbatar da rasuwarta. An birne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Yanzu-yanzu: Yan Nigeria sun dauki mataki akan mawaki Rarara

”Daily trust ta ruwaito cewar Naja’atu ta shiga banɗakin ɗalibai mata na kwalejin Gubi da safiyar Juma’a domin yin wanka ta kuma shirya ta tafi aji.

“Ta shirya kamar yadda ta saba domin zuwa ajin safe kafin ta shiga baɗakin wankan. Ta kawo kayan da za ta saka idan ta fito daga wankan, ta ajiye su a gefen gadonta,” a cewar abokiyar kwananta.

Talla

Haka kuma, a cikin sakon ta’aziyya, Kungiyar Ɗalibai ta ATBU, ta bakin Sakataren Ƙungiyar, Kwamared Danladi Zakiru, ta bayyana marigayiyar a matsayin ɗaliba mai ƙwazo wadda za a yi matukar kewarta a tsakanin ɗaliban jami’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...