Sanata Kawu Sumaila Zai Dauki Nauyin Karatun Mahaddata Qur’ani 100 a Kano ta Kudu

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

 

Sanatan Kano ta kudu Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce zai sake daukar nauyin karatun wasu Malamai guda 100 daga yankin, wadanda za su koyo harkokin Addinin Musulunci .

A cikin sanarwar da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai na 2 Abbas Adam Abbas ya aikowa kadaura24, yace Sanata Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne ya yin taron makon ilimi na waraka na shekarar 2024.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a baya Sanata Kawu Sumaila ya dauki nauyin karatun wasu Matasa 550 wadanda suka fiti daga kananan hukumomin Kano ta kudu.

Talla
Talla

 

Ya nuna alfahari da kaddamar da sabon shirin bayar da tallafin karatu da nufin tallafa wa malaman addinin Musulunci 100 a Kano ta Kudu.

Sanata Sumaila ya jaddada muhimmiyar rawar da ilimi da kiwon lafiya ke takawa wajen bunkasa ci gaban al’umma. Sannan ya bayyana muhimmancin taimakawa mutane da basu ilimi a mahanga ta Addinin Musulunci.

Ni Dan Siyasa Ne Ba Dan Kungiya ba – Sanata Kawu Sumaila

Sanata Kawu ya ce manufar bayar da tallafin karatu ga malaman addinin Musulunci guda 100, ita ce samar da kwararrun malaman addinin Musulunci a fannoni daban-daban kamar Da’awa, Shari’a, da wa’azin addinin Musulunci.

Ya kara da cewa yana da manufar baiwa matasa damar zama shugabanni da kuma dogaro don shawo kan kalubalen da ke fuskantar al’ummar.

 

Talla

“Alkawarinmu na inganta ilimi da lafiya yana nan daram ,” inji Sanata Sumaila. “Dole ne mu yi aiki tare don karya tsarin rashin ci gaba tare da samar da makoma wadda kowane mutum zai sami damar ci gaba.”

Ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su goyi bayan wannan shiri mai albarka, domin zai taimaka sosai wajen inganta rayuwar al’ummar yankin Kano ta kudu.

Sanata Sumaila ya jaddada kudirin sa na ganin an kyautata rayuwar al’ummar mazabar sa da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...

Kungiyar Karamci United Family ta Karrama Shugaban gidan Radiyon Pyramid Saboda Taimakawa Al’umma

Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM Dr. Garba Ubale...

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...