Ra’ayin Adnan Mukhtar
Akwai bukatar samun lasisi da izini don farawa aikin matatar mai a Najeriya, wadanda mutane da yawa basu sani ba, kuma ba su damu da su sani ba.
Dambarwar baya-bayan nan kan matatar dangote da hukumomi irin su NMDPRA da NNPCL ya bude idanu mutane da yawa a Nigeria kan harkar mai da iskar gas da kuma abubunwan da ake bukata kafin matatar mai ta fara aiki gadan-gadan a Nigeria .
Bari in fara da manyan guda uku wadanda su ne: Lasisi don kafa matatar mai da lasisi domin gina matatar sai kuma neman izinin matatar ta fara aiki.
Dangote ya chanchanci lasisi guda biyu amma kuma ya same su, amma ba shi da guda daya, shi ne Lasisin fara cikakken aiki.

Amma ’yan Najeriya za su yi wannan tambayar me yasa ya sami biyu amma ba shi da daya? saboda rashin sanin ka’ida da harkokin kasuwancin mai. Rashin fahimtar kalaman Shugaban NMDPRA ko rashin sanar da al’umma ainahin abun da ya fada shi ne abun da ya kawo rudanin .
Wannan ne ya sa na yanke shawarar yin wannan rubutun don amfanin duk ‘yan Nijeriya da ba su da masaniyar fasahar aikin matatar mai .
Me ya sa za ku ce Dangote ba shi da lasisin yin aiki alhali mun san yana aiki? Wannan tambaya ce da ‘yan Najeriya da dama su ke yi.
Har yanzu Dangote ba shi da izinin aiki a matatarsa, ya san wannan shi da mutanen dake kusa da shi. Misali, lokacin da Najeriya ke baiwa OPEC bayanan watan Maris/Afrilu, ba ta bayar da rahoton cewa matatar Dangote ta fara aiki ba saboda Dangote ba shi da lasisin fara aiki duk da cewa matatar ta fara aiki tun a watan Janairu.
Kowanne abu guda ɗaya a cikin matatar man sai za a gwada shi domin tabbatar da ingancinsa kafin ba da wannan lasisin aiki na ƙarshe (LtO).
Amma, idan aka yi la’akari da girman matatar Dangote da kuma matsin tattalin arzikin da muke fama da shi na matsalar makamashi, shi yasa aka bar shi ya yi aiki.
Gwamnatin Jigawa za ta hada hannu da Saudiyya don inganta makarantun allo
An yanke shawarar ba da lasisin fara aiki ga Dangote zuwa kashi-kashi tare da ba da izinin farawa ga rukunin a kowane lokaci, har zuwa lokacin da za a je matakin karshe da za a amince a bashi izinin fara aikin.
Wannan tsari yana kusan kashi 45% cikin 100, duk da cewa mafi yawan manyan na’urorinsu har yanzu ba su fara ba.
Sashin sarrafa danyen mai na Dangote shi ne babban rukunin a kashi na farko wanda aka fara a watan Janairu, inda ya fara samar da naphtha, jet, man fetur, dizal, da sauran mai.
Aikin da ta fara a watan farkon watan Janairu ya kasance ba mai yawa ba, bai wuce 80,000 bpd ba har kusan kusan watan Maris. Don haka, ba a iya cika tankunan ajiya dake cikin matatar, kuma sana’ar na iya fara ajiye kudi don biyan basussuka, kuma an baiwa matatar izinin fitar da shi zuwa kasashen waje, wanda aka fara a watan Maris, da kuma damar sayar da dizal ga yan kasuwar cikin gida wanda ya fara a watan Afrilu.
Dangote ya bukaci sayar da dizal a Najeriya saboda yawan sinadarin sulfur a cikin dizal dinsu da yawansa ya kai tsakanin 650ppm zuwa 1,200ppm. Kar ku manta sashin tace sulfa na matatar bai fara aiki ba .
Amma a cikin watan Maris, NMDPRA ta fara tabbatar da sinadarin sulfur bai wuce 200ppm a dizal din da za a shigo da shi kasar nan ba. Don haka, a daidai wannan lokaci ne aka dagawa Dangote kafa ya sayar da man dizal wanda bai haura 1,000ppm, masu shigo da kayan ba a basu damar shigo da abin da ya wuce 200ppm ba. Shin gwamnatin tarayya tana adawa da Dangote kenan ?
Ku sani cewa a tsakanin shekarar 2003 da Najeriya ta karya kasuwar dizal dinta, sai aka fara shigo da dizal din Turai, kuma wanda ake shigo da shi daga Turan zai iya zama mai guba sau 200 fiye da dizal din da aka tace daga danyen da aka sata a yankin Neja Delta ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani.
Dizal din Turai ya yana da matsala ba kawai a Najeriya ba har ma da duk kasashen nahiyar. Don haka Najeriya ta tsaya tsayin daka don ganin ta yaki wannan matsala, tun daga shekarar 2016, don rage yawan sinadarin sulfur a cikin kayayyakin man fetur. Manufar ECOWAS yanzu ita ce ya zamana mafi yawan sinadarin sulfar Kar ya wuce 50ppm nan da 2025.
Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria
Haka kuma an yi kokarin hana fitar da gurbataccen man diesel daga nan zuwa Afirka, musamman daga cibiyar Amsterdam-Rotterdam-Antwerp, da farko daga kasar Holland sannan kuma kasar Belgium.
Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Ecowas ta 2020 wacce ta amince da sinadarin sulfar kar ya wuce 50ppm.
Daga nan Dokar Masana’antar Man Fetur ita ma ta amince da hakan cikin dokokinmu a 2021.
Matsayar da aka cimma ta hana matatun mai na Ecowas, yin amfani da sinadarin sulfar da ya wuce 50ppm a matatun dake Ivory Coast, Ghana, Nijar, Najeriya da Senegal.
Abin lura shi ne iya adadin sinadarin sulfar a cikin mai shi ne ita adadin dattin da Kuma arahar sa.
Amma dizal din Dangote ana sayar da shi ne a kan farashi daidai da yadda ake samun tsaftataccen man dizal da ake shigo da shi, wanda hakan riba ce ga kasuwancin Dangote.
Idan za a iya tunawa farashin kudaden waje sun yi tafin gwauron zabi musamman a ƙarshen watan Fabrairu da farkon watan farkon Maris. Amma matsin lambar sai an dawo da darajar Naira bai Dangote ya rage farashin dizal din sa.
Shirun da mutane su ka yi shi ya baiwa Ɗangote damar fitowa yana babatu, har ake ganin ana cutar shi.
Adnan Mukhtar Dan Jarida ne kuma me sharhi akan alamuran yau da kullum. Za a iya samunsa a shafin ta email a adnanmukhtaradam@gmail.com