Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata, jarirai da kananan yara na shekarar 2024 a hukumance.
Hakan na kunshi ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
A jawabinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa makon lafiyar mata da kananan yara na da burin inganta kiwon lafiyarsu ta hanyar mayar da hankali da daukar matakan rigakafi da magance cutar da ke addabar iyaye mata da yara.

Ya kara da cewa, taron na tsawon mako guda wata dama ce ga mata da kananan yara domin su kara samun kulawa ta hanyar tsarin kiwon lafiya da ake da su, wanda ke kara karfafa ayyukan kula da lafiyar mata da kananan yara kyauta da ake samu a kanana da manyan asibitocin jihacin da ke jihar.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar al’ummarta.
Yanzu-yanzu: Yan sanda sun bayyana sharudda ga masu son shiga zanga-zanga a Nigeria
Ya nanata kudurin gwamnatinsa na rage mace-macen mata da kananan yara da kuma shawo kan cututtukan da za a iya magance su kamar su zazzabin cizon sauro, HIV, da tarin fuka.
Tun da farko kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa Manufar makon kula da lafiyar mata da kananan yara shi ne samar da cikakkiyar kulawa ga mata masu juna biyu tun daga daukar ciki har haihuwa da kuma tabbatar da jin dadin jarirai da yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Dakta Labaran ya bayyana jin dadinsa da yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajirce wajen kula da fannin kiwon lafiya tare da bada tabbacin cewa ma’aikatan lafiya a jihar Kano sun kuduri aniyar samar da ayyuka masu inganci ga al’umma.
Taron ya sami halartar wakilin Sarkin Kano, Turakin Kano kuma Hakimin Dala, Alhaji Abdullahi Lamido Sanusi, da wakilan kungiyoyin ba da tallafi a bangaren lafiya da suka hada da NPHCDA, UNICEF, WHO, ALIVE & THRIVE, da MSF.