Dalilan da suka sa NLC ta amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Date:

 

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta NLC sun sanar da amincewarsu da naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan ƙasar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya amince da sabon albashin a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.

Talla

Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce sun amince ne da tayin N70,000 saboda akwai abubuwan da ke ƙunshe da ya kira na ƙarfafa guiwa.

Sarkin Gaya Ya Karbi Takardar Kama Aiki a Karo Na Biyu Daga Gwamnan Kano

Ƙungiya ta ce abin da ya ƙara ƙarfafa mata guiwa na amincewa da tayin shi ne alƙawalin da shugaban ƙasar ya ɗauka na sake duba albashin duk bayan shekara uku maimakon shekara biyar, kamar yadda mataimakin shugaban Kabiru Adamu Minjibir ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa.

Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya ayyana mafi ƙarancin albashi

“Sannan gwamnati za ta bayar da manyan bas bas masu ɗaukar mutum 100 wanda zai rage wa ma’aikata wahalar tafiye-tafiye,” in ji shi.

Tun janye tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi, ta shiga takun-saka da ƙungiyoyin ƙwadago, inda suka nemi ƙarin albashi da ya zarta kashi 300 cikin 100 sakamakon tsadar rayuwa da janye tallafin ya jefa ƴan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...