Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sake maka tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a gaban Babbar kotun jihar, bisa wasu zarge-zarge masu alaka da kudade.
A cikin takardar karar mai lamba K/143c/24, gwamnatin jihar ta zargi Ganduje da tsohon kwamishinan shari’a, Musa Lawan da laifin hada baki da kuma karkatar da dukiyar jama’a.
Gwamnatin Kano ta zargi Gwamna Ganduje da Lawan da yin zagon kasa.
A cikin takardar tuhumar, gwamnatin jihar ta ce tana da niyyar gabatar da shaidu hudu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba sanya ranar da za a gurfanar da su a gaban kotu ba.
Da dumi-dumi: Majalisar dokokin jihar kano ta kirkiri sabbin masarautu
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar 4 ga watan Afrilu ne gwamnatin Kano ta kai karar Ganduje da matarsa, Hafsat Umar da wasu mutane shida a gaban babbar kotun Kano.
Sauran shidan sun hada da dan Ganduje, Umar Abdullahi Umar, Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd., Safari Textiles Ltd., da Lesage General Enterprises.
A lokacin da aka ci gaba da sauraren karar, mai shari’a Amina Aliyu ta nuna damuwarta kan yadda wadanda ake tuhumar suka kasa gurfana a gaban kotun duk da cewa an bi wasu hanyoyin domin isar musu da sammacin kotun za su yi aiki da su.
Lauyoyin masu kara, karkashin jagorancin Adeola Adediyo, sun bukaci kotun da ta ba da izinin kamo Ganduje, da matarsa, da wasu mutane shida.