UNICEF ta yabawa Gwamnan Kano bisa baiwa harkokin Ilimi fifiko a Jihar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yabawa Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa wajen inganta fannin ilimi a Kano.

Shugabar asusun a Nigeria Christain Munduate, ta bayyana hakan ranar alhamis, a gidan gwamnatin kano.

Talla

Ta ba da tabbacin cigaba da samar da hadin gwiwa mai dorewa a tsakanin UNICEF da jihar Kano, kara ciyar da fanni ilimi a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.

Da dumi-dumi: Doguwa Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

Misis Munduate ta jaddada cewe UNICEF za ta cigaba da tallafawa gwamnatin jihar musamman a bangarorin kiwon lafiya da ilimi, inda ta jaddada wajibcin jihar Kano wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da kudade na ayyukan samar da abinci masu gina jiki ga yara.

A nasa jawabi, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba wa UNICEF da sauran hukumomin bada tallafi, inda ya bayyana cewa ya baiwa ilimi da lafiya a muhimmanci, don haka yana bukatar karin tallafi don dorewar aiyukan da ya dauko.

Iftila’i: Makaranta Ta Rushe Da Dalibai Suna Zana Jarabawa

Gwamna Yusuf ya nuna rashin abinci mai gina jiki da cutar shan inna a matsayin matsalolin kiwon lafiya, musamman ma yara da sauran al’umma masu karamin karfi.

Da yake bayani dalla-dalla irin nasarorin da aka samu a fannin ilimi a gwamnatinsa, Gwamna Yusuf ya jaddada himmar gwamnatinsa wajen samar da muhimman ababen more rayuwa, kayayyakin ilimi, ajujuwa na zamani, da shirye-shiryen horar da malamai, da samar da yanayi mai kyau don inganta harkokin koyo da koyarwa.

Bugu da kari, a fannin kiwon lafiya, Gwamna Yusuf ya jaddada kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da samar da aikin jinya na kyauta ga mata da yara, gyaran asibitoci, da samar da kayayyakin kiwon lafiya da kayan aikin da ake bukata.

Gwamna Yusuf ya bayyana kudirin jihar na rubanya gudunmawar tallafin da takwarorinsu ke bayarwa idan aka kwatanta da jihar Jigawa wajen yaki da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...