Ginin gidajen da gwamnatin Tinubu ke yi ya samar wa matasa da dama aiyukan yi – Ministan Gidaje

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Ministan Gidaje da Raya Birane Arc Ahmad Musa Dangiwa, ya bayyana cewa shirin “Renewed Hope Housing” an shirya shi ne domin samar da gidaje don samar da ayyukan yi, inganta rayuwa da bunkasa tattalin arzikin ‘yan Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne ta bakin karamin ministan gidaje da raya birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a yayin kaddamar da harsashin ginin gidaje guda 250 na rukunin Renewed Hope na fadar shugaban kasa a Makurdi babban birnin jihar Benue a ranar Juma’a.

“Ina so in bayyana cewa a karkashin tsarin sabunta fata na mai girma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, GCFR, mu a ma’aikatar gidaje da raya birane ta tarayya, mun damu sosai wajen baiwa ‘yan Najeriya damar inganta tattalin arzikin su,” in ji Ministan

Dalilan da suka sa lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero su ka fice daga shari’ar dambarwar masarautar Kano

A cikin sanarwar da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24, Ministan ya kara da cewa an ware wa aikin kuɗaɗe sosai daga karin Naira biliyan 50 na shekarar 2023 da shugaban ƙasa ya amince wa ma’aikatar don tabbatar da cigaban kasa .

Talla

Minista Gwarzo ya bayyana cewa samar da filayen da Ake ginin wurare masu daraja a kowacce jiha shi ne babban sharadi na samar da shirin Renewed Hope Housing Project, inda ya ce Jihohi 12 da ake yin aikin cikin karin kasafin kudin shekarar 2023 su ne wadanda suka fara bayar da filayen, yayin da su kuma wadanda suka yi jinjirin ba da filayen zasu kasance a cikin Kasafin Kudin 2024 na Ma’aikatar.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu ana ci gaba da aiki a kowane wuraren da aka fara kaddamar da gine-gine a fadin Jihohin kuma ana shirin kammala dukkan gidajen nan da watanni biyu masu zuwa kuma a samar wa ‘yan Najeriya daidai da bukatar Shugaban kasa na samar da gida mai araha ga dukkan ‘yan Najeriya.

Yadda majalisar wakilai ta tasamma baiwa Sarakuna iko a kundin tsarin mulki

Ministan ya umarci ’yan kwangilar da su tabbatar sun yi gini mai inganci, yana mai jaddada cewa ba za lamunci yin gini maras inganci ba, kuma yace zasu dauki matakin doka akan duk dan kwangilar da ya yi ha’inci.

Don haka, Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa an samar da wasu zabuka daban-daban don baiwa duk wanda ke da hanyar samun kudin shiga ya mallaki wadannan gidaje idan an kammala su.

Ya godewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa yadda ya yi hangen nesa wajen kawo tsarin da zai baiwa yan Nigeria damar mallakar gidaje cikin sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...