Yadda majalisar wakilai ta tasamma baiwa Sarakuna iko a kundin tsarin mulki

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban Majalisar Wakilan Nigeria Tajuddeen Abbas, ya tabbatar wa sarakunan gargajiya da ‘yan Najeriya cewa majalisar ta 10 ta kuduri aniyar samar da ayyukan yi ga sarakuna da ba da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi a gyaran kundin tsarin mulkin kasa da ake yi.

Abbas ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din da ta gabata bayan wani taron tattaunawa kan rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen ci gaban kasa.

Ya bayyana cewa majalisar ta kafa wasu kwamitoci na musamman guda biyu domin tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomi tare da baiwa Sarakunan gargajiya matsayi a kundin tsarin mulki.

Dalilan da suka sa lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero su ka fice daga shari’ar dambarwar masarautar Kano

“Majalisa ta 10, karkashin jagorancina, za ta yi kokarin ganin ta samawa sarakunan gargajiya matsayi aikin gyaran kundin tsarin mulkin mu. Duk da yunkurin da aka yi a baya, mun yi imanin cewa Sarakunan gargajiya su ne kashin bayan al’ummarmu,” inji Abbas.

Talla

A jawabinsa Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya ce idan za a iya tunawa masarautun gargajiya a Najeriya sun samo asali ne don samar da ingantaccen jagoranci ga al’ummomi.

Ya kara da cewa turawan mulkin mallaka sun yi amfani da waɗannan masarautun don gudanar da mulki saboda mahimmancin su.

Kafin Zuwan Gwamna Abba Kabir Yan Fansho a Kano Suna cikin Mawuyacin Hali – Sarki Sanusi II

Ya koka da cewa rashin basu iko a kundin tsarin mulki ya haifar da mummunan tasiri ga al’ummomi da karuwar laifuka da rashin tsaro a cikin al’umma.

“Muna kira ga wannan Majalisar da ta yi amfani da wannan lokaci da take gyaran kundin tsarin mulkin Nigeria wajen sake baiwa Sarakunan gargajiya iko domin mu taimaka wa gwamnatoci wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya,” in ji Abubakar.

Yakubu Maikyau, SAN, shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), ya bukaci majalisar kasa ta 10 ta ba da goyon bayan doka ta hanyar baiwa Sarakunan gargajiya iko a kundin tsarin mulkin kasa.

Ya yaba wa shugaban majalisar kan yadda ya bayar da shawarwari ga ayyukan masarautun gargajiya a cikin kundin tsarin mulki tare da yin kira da a samar da tsaro ga masu rike da sarautun gargajiya, domin gujewa abubunwan da tasirin yan siyasa ke haifar musu.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...