Daga Rahama Umar Kwaru
Sabon kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Kano Salman Dogo Garba ya ba da tabbacin yin duk mai yiwuwa domin samar da isasshen tsaron rayuka da dukiyoyi al’umma.
CP Salman Lawal Dogo ya bayyana hakan ne a yayin bikin kama aiki da kuma yin bankawa da tsohon kwamishinan ‘yan sandan Najeriya AIG Mohammad Hussein Gumel wanda ya samu karin girma a kwanakin baya, wanda aka gudanar a jami’ar Mess Bompai Kano.
’Yan Sanda Sun Kori ’Yan Tauri Daga Fadar Sarkin Kano
Ya nemi goyon baya da hadin kai daga jami’an rundunar ‘yan sandan Kano da sauran jama’a, da nufin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Yayin da yake jawabi kwamishinan mai barin gado AIG Mohammad Hussein Gumel ya yabawa manya da kananan jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano bisa hadin kan da suka ba shi a lokacin da yake rike da mukamin CP a Kano, inda ya jaddada cewa hakan ne ya sanya ya samu nasarori masu yawa a Kano.
Gwamnan Sakoto Na Shirin Tsige Sarkin Musulmi —MURIC
AIG Mohammad Hussein Gumel ya bukaci manya da kananan jami’an Rundunar da su baiwa sabon kwamishinan hadin kai don shi ma ya sami nasarar inganta harkokin tsaro a kano.
A yayin bikin mai cike da ban sha’awa, kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kano ta ba da lambar yabo ga kwamishinan mai barin gado, AIG Mohammad Hussein Gumel bisa bajintar da ya nuna a lokacin da yake jagorantar rundunar a jihar kano.