Daga Kamal Yahaya Zakaria
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi wasu ‘yan adawa a Kano da rikitawa gwamnati na tsawon shekara guda.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron farfado da harkokin ilimi a jihar Kano.
Ya ce, “Bari in fara da taya shi ( Abba Kabir Yusuf) murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Muna so su sani cewa gwamnan yana aiki tun daga ranar farko da ya zama gwamnan jihar Kano .
Zargin Rashawa: Kwankwaso Ya Maka Hukumar EFCC A Gaban Kotu
Duk da cewa gwamnan ya gamu da kalubale a shekararsa ta farko a gwamnati, jim kadan bayan ya ci zabensa, maƙiyan jihar Kano suka kai shi kotu ta farko, suka tafi har kotun daukaka kara har zuwa Kotun Koli.
“Hatta makiya sun san cewa shi ya ci zaɓen sa, Amma sukai ta kokarin sai sun kwace masa kujerar sa ta karfin ciya kawai saboda sun yi imanin cewa suna da gwamnatin tarayya . Duk da haka, gwamnan yana aiki, amma kuma yana ta gamuwa da cikas Kuma duk da hakan bai daina aiki ba.
“A gaskiya wannan ya tuna min halin da muke ciki a wa’adina na biyu bayan watanni biyu da rantsar da ni a matsayin gwamna, mun sha fuskanci hare-haren Boko Haram a masallatai, ana kai hare-hare a kasuwanni, ofisoshin ‘yan sanda, makarantu , amma duk da haka sai da muka mai da hankali muka ga mun yi nasara.”
Daily Trust