Muna Kira ga Gwamnatin tarayya da ta kammala aiyukan da aka fara a Arewacin Nigeria – NRO

Date:

Kungiyar Northern Reform Organization ta bukaci wakilan Arewa a majalisar zartarwar ta kasa da majalisar kasa da su himmatu don ganin gwamnatin tarayya ta kammala aiyukan da ba ta kammala ba a yankin.

 

“Akwai muhimman aiyuka da ya kamata gwamnatin tarayya ta kammala su, wadanda zasu taimaka sosai wajen ciyar da yankin Arewacin Nigeria gaba”.

 

Fargaba a Kano: Sarki Sanusi da Sarki Aminu na shirin gabatar da Sallar Juma’a a Masallacin Guda

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wani sakon taya murnar cika shekara da hawa mulkin ga shugaban kasa Bola Tinubu da daraktan yada labaran kungiyar Mahmoud Adnan Audi ya sanyawa hannu kuma ya turowa kadaura24.

 

Sanarwar ta ce akwai aiyuka da suka hadar da aikin kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta da aikin yashe Kogin River Niger da aikin hakar danyan man da aka samo a kolmani a iyakar Bauchi – Gombe da dai sauransu.

Yan Sanda sun magantu kan shirin Sarki Aminu da Sarki Sanusi na yin sallar juma’a a masallaci guda

Sanarwar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ya mai da hankali wajen kammala aikin titin kano zuwa Abuja da kuma na Kano zuwa Katsina da na Legos zuwa illori zuwa kaduna da sauran su.

 

Sanarwar ta kuma kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta magance matsalolin tsaro da suka addabi wasu daga cikin jihohin Arewacin Nigeria.

 

Ta kuma taya shugaban ƙasa Bola Tinubu murnar cika shekara daya akan karagar mulkin Nigeria.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...