Daga Sani Idris Maiwaya
Tsohuwar tauraruwar Kannywood Fatima Usman wadda aka fi sani da Fati Slow ta rasu a jiya litinin.
Fati slow dai dai tsohuwar jaruma ce da ta bada gagarumar gudunnawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta kannywood a shekarun baya.
Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano
Shugaban Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Abba El-Mustapha ne ya tabbatar da rasuwar jarumar a shafinsa na Facebook ranar Talata.
Gwamnan Kano ya Nada Mai rikon Mukamin Manajan Daraktan ARTV
Ita ma jaruma mansura Isa ta bada labarin rasuwar fati slow,Inda ta ce ta rashi ne a habasha kuma za a gudanar da zaman makoki a gidan su dake unguwa uku.
Muna addu’ar Allah ya gafarta mata yasa aljanna ta zamo makomarta da mu baki daya.