Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar rushe masarautun da Ganduje ya Samar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Majalisar dokokin jihar kano ta amince da dokar soke karin Masarautu guda 4 a jihar.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a Shekarar 2019 majalisar dokokin jihar kano ta amince da dokar kara masarautu guda 4 a jihar, Inda kuma gwamnan Kano na wancan lokacin Abdullahi Umar Ganduje ya sanya mata hannu kuma ta zama doka.

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da dokar majalisar masarautu ta Kano 2024 bayan kammala karatu na uku.

 

Dokar ta soke kafa sabbin masarautu guda 4 a jihar.

Dokar ta ce duk ofisoshin da aka kafa a karkashin dokar da aka soke, sabuwar dokar ta rushe su an rushe su .

Haka kuma duk hakimai da aka daukaka ko aka nada a karkashin dokar da aka soke za su koma kan mukamansu na baya.

Shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazabar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya gabatar da kudirin gyaran sabuwar dokar a gaban zauren majalisar dokokin jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...