Hasashen yanayin da zai kasance yau Asabar a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau Asabar 18-05-2024 dai-dai da 10 ga watan Dhul-Qada 1445 A.H , idan Allah ya so za’a sami zafin rana a jihar Kano wanda zai kai 41 bisa ma’aunin zafi, tare da dumamar yanayi da zai kai
57 cikin dari.

Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.

Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 41 bisa ma’aunin zafi.

Matashin da ya bankawa masallata wuta a Kano ya bayyanawa yan sanda dalilinsa na yin aika-aikar

A jihar Kano dai babu yiwuwar samun ruwan sama a yau

Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.

Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.

Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 36 bisa ma’aunin zafi.

Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 35 bisa ma’aunin zafi.

Dalilin da yasa nake kokarin hada kai da Peter Obi – Atiku Abubakar

Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.

Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 42 bisa ma’aunin zafi .

Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 42 bisa ma’aunin zafi.

ABIN LURA: Hasashen ka iya chanjawa a kowanne lokaci.

Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...