Matashin da ya bankawa masallata wuta a Kano ya bayyanawa yan sanda dalilinsa na yin aika-aikar

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ’yan sandan jihar kano ta ce sun kama wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 da ake zargin ya cimma wa mutane wuta a lokacin da suke sallar asuba a Jihar Kano.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa kimanin mutane 30 ne suka sami raunika daban-daban sakamakon wuta da ake zargi wani matashi da ba a san ko wa nene ba, ya bankawa musu wuta a lokacin da suke tsaka da yin Sallar asuba.

Iftila’i: Ana fargabar sama da mutane 30 sun kone suna tsaka da sallar asuba a wani masallaci a Kano

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda jama’a na rundunar yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Sanarwar ta ce Shafi’u Abubakar ya bayyana musu cewa binciken farko ya nuna matashin ya yi wannan aika-aika ne a sakamakon rikicin gado.

Abduljabbar ya dakatar da lauyan dake kare shi a kotun daukaka kara ta Kano

” Akwai guda cikin yan uwana da suka hana ni Gadon na a cikin masallacin shi yasa na yi wannan abun sakamakon kokarin cutata da suke so su yi”. A cewar

Yan sandan sun ce suna cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...