Daga Halima Auwalu Abdullahi
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Juma’a ya bi sahun takwarorinsa na Arewa maso Yamma yayin wani taro da jami’an Majalisar Dinkin Duniya a Abuja.
Wadanda suka halarci taron tare da Gwamna Yusuf sune Gwamnonin jihar Kaduna, Uba Sani; Jihar Katsina, Umaru Dikko Radda; Jihar Jigawa, Muhammad Namadi; jihar Zamfara, Dauda Lawan Dare da mataimakin gwamnan jihar Sokoto wanda ya wakilci gwamnan.
Ganawar da gwamnonin suka yi da jami’an majalisar dinkin duniya ya tilastawa ta hanyar bayyana kalubalen ci gaban da ke addabar jihohin yankin da kuma bukatar gaggawar neman shiga tsakani na kasa da kasa a yankin a sassan da suka shafi tattalin arziki.
Hasashen yanayin da zai kasance yau Asabar a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, ya aikowa kadaura24 ya bayyana cewa gwamnonin yankin sun yunkuro domin kawo cigaba a yankin Arewa maso Yamma.
Sanarwar ta jaddada cewa taron hadin gwiwa na farko da gwamnonin Arewa maso Yamma suka yi da jami’an Majalisar Dinkin Duniya ya ba da damar samun damammaki wajen tattauna batutuwan da suka shafi kiwon lafiya, ilimi, tsaro, noma da sauran muhimman batutuwa da suka cigaban yankin.
Kantoman Karamar hukumar Bichi ya ba da umarni ga wadanda aka baiwa filaye a yankin
A cikin jawabinsu na bai daya, gwamnonin Arewa maso Yamma sun nemi majalisar dinkin duniya ta gaggauta daukar matakai ta hanyar hukumominta don ceto yankin daga matsalolin da ke barazana ga rayuwar al’ummar yankin.
Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, a kwanan nan Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya wa Gwamnonin Arewa Maso Yamma wani taron tattaunawa kan harkokin tsaro domin fadada ilminsu kan yadda zasu karfafa daukar matakan kariya da magance matsalolin tsaro dake faruwa a yankin.
Taron na kwanaki uku na Amurka, wanda ya samu halartar Gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Plateau, an tsara shi ne domin tallafa wa jihohin su magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
A karon farko cikin shekara ta 2023 gwamnoni arewa maso yamma sun aminta su fito da wani tsari da zasu rika tafiya akan sa domin ciyar da yankin gaba ta fuskokin daban-daban karkashin jagorancin gwamnan jihar Katsina Ummaru Dikko Radda.