Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kantoman karamar hukumar Tudun wada a jihar kano Dr. Umar Isah Rugu-Rugu ya jagoranci raban tallafin kudi naira dubu hamsin ga mata 100 domin su ja jari su dogara da kawunan su .
Da yake jawabi yayin tallafin Dr. Umar isah rugu-rugu ya yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin mai girma gwamna Alh. Abba kabir yusuf bisa yadda ta ke kokarin raba irin wannan tallafin ga Al’umma duba da halin matsin rayuwa da Al’umma suka tsinci kansu ciki.
Hasashen yanayin da zai kasance yau Asabar a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Dr. Umar isah rugu rugu yakara da cewa ” An baku wannan jali ba dan komai ba sai domin aje a cigaba da gudanar da sanao’i wadanda basa sana’ar kuma su nemi sana’o’in da za su yi domin kowa ya samu kuma ya dogaro da kansa.
Kantoman Karamar hukumar Bichi ya ba da umarni ga wadanda aka baiwa filaye a yankin
“Muna fatan za kuyi dukkanin mai yiwuwa wajen amfanar da kanku da sauran al’umma kuma Muna fata wannan tallafin zai zamo silar arzin ku”.
Rugu-rugu yaja hankalin al’ummar yakin musamman wadanda basu samu a wannan karon ba da su yi hakuri wannan shi ne karon farko kuma za’a cigaba da bayar da irin wadannan tsare tsaren a nan gaba .