Daga Nura Adam Lajawa
Rohotannin da ke Isa ke jaridar kadaura24 na tabbatar da cewa akalla mutane 7 sun rasu daga cikin mutane kusan 30 da aka Cinnawa wuta a garin larabar abasawa dake karamar hukumar Gezawa a Kano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wani matashi ya banka wuta kan wasu masallata a garin larabar abasawa yayin da suke tsaka da sallar asuba ta wannan rana ta laraba.
Iftila’i: Ana fargabar sama da mutane 30 sun kone suna tsaka da sallar asuba a wani masallaci a Kano
Wakilin kadaura24 da a yanzu haka yake garin ya tabbatar mana cewa tuni an yi jana’izar mutane biyu da suka fara rasuwa cikin mutanen da suka konen.
Matashin da ya bankawa masallata wuta a Kano ya bayyanawa yan sanda dalilinsa na yin aika-aikar
Yanzu haka kuma mutane biyar sun kara mutuwa wadanda aka dakon kai kawawwakin su daga asibitin Murtala zuwa garin domin yi musu sutura kamar yadda Addinin Musulunci ya yi tanadi.
Tuni dai yan sanda suka tabbatar da kama wanda ake zargi da cinna wutar, Inda ya fada musu cewa yayi hakan ne saboda kokarin da yan uwansa ke yi na hana shi gadonsa.