Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau litinin 13-05-2024 dai-dai da 5 ga watan Dhul-Qada 1445 A.H , idan Allah ya so za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 40 bisa ma’aunin zafi.
A jihar Kano dai akwai yiwuwar samun ruwan Sama da Kaso 20 cikin 100.
Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.
CBN Ya Fitar Da Jerin Sunayen Bankunan Ajiya Masu Lasisi a Nigeria
Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 40 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.
Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.
Abubuwan da ya kamata yan Arewa su yi don amfana da mulkin Tinubu – Kwankwaso
Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 35 bisa ma’aunin zafi.
Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 34 bisa ma’aunin zafi
Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 39 bisa ma’aunin zafi .
Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.
Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance