Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau lahadi 12-05-2024 dai-dai da 4 ga watan Dhul-Qada 1445 A.H , idan Allah ya so za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 40 bisa ma’aunin zafi.
A jihar Kano dai akwai yiwuwar samun ruwan Sama da Kaso 20 cikin 100.
Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.
Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature ya tallafawa mata 100
Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 40 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.
Wani Yaron Ya Sayar Da Ζodarsa Ya Sayi Wayar Hannu
Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.
Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 34 bisa ma’aunin zafi.
Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 32 bisa ma’aunin zafi
Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 41 bisa ma’aunin zafi .
Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.
Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance