Gwamnatin Kano Zata Fara Karrama Malaman Makaranta Masu Kwazo

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban Hukumar Ilimin dai daya na jiha, Malam Yusif Kabir ya bayyana kudurin hukumar wajen yabawa malaman makaranta masu nuna kwazo da rike aikinsu bisa amana ta hanyar karramasu da takardar yabo da kuma sanya su cikin duk wani tsarin inganta rayuwar ma’aikaci.

Shugaban ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziayara a makarantar fimare ta Danzaki dake yankin Karamar Hukumar Gezawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Balarabe Danlami Jazuli kuma aka aikowa kadaura24.

Hasashen yanayin da zai kasance yau Litinin a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Malam Yusif Kabir ya ci gaba da cewa makasudin ziyarar shi ne don duba yadda malaman makarantar suke gudanar ayyukansu, sai ya yabawa malaman bisa yadda suke gudanar da ayyukansu bil hakki.

Kazalika shugaban ya yi alkawarin bayar da bashin sayen abin hawa da hukumar take bai wa malamai masu aiki tutkuru, in da ya sanya sunan Malam Alkasim Usaini da Malama Maryam Ibrahim na wannan makaranta ta Danzaki a matsayin wadanda zasu amfana da wannan shiri a matsayin wata godiyar shugaban gare su ta gudanar da aiki tukuru.

Yan sanda a Kano na bincike kan mutuwar jami’in kwastam da ake zargin ya kashe kansa

A wani ci gaban Shugaban Hukumar ya ziyarci sakatariyar ilimi ta Karamar Hukumar Gezawa, inda anan ya nuna bacin ransa, kan yadda ya tarar da sakataren ilimi da kananan ma’aikata kadai ne su ka je aiki a lokacin da ya isa sakatariyar ilimin.

Malam Yusif Kabir ya ja kunne manyan ma’aikata dake aiki a sashen, su sauya halayyarsu ta makara da fashin zuwa aiki ko su hadu da fushin hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...