Daga Aliyu Abdullahi Fagge
Rahotanni da muke samu yanzu na nuna cewa jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai samame kasuwar Chanjin kudaden waje ta WAPA dake Kano .
Wani Dan Kasuwar da kadaura24 ta zanta da shi Bisa sharadin sakaye sunansa, yace jami’an hukumar ta EFCC a yau litinin sun kai samame har sau uku a wannan rana.
Hasashen yanayin da zai kasance yau Litinin a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
” Da fari kafin a Fara hada-hada sosai a kasuwar da misalin karfe 12 na rana sai ga jami’an hukumar ta EFCC chan wajen karfe 2 kuma suka sake dawowa, awa daya bayan tafiyar su kuma sai suka sake dawowa cikin kasuwar, hakan yasa duk muka gudu”. A cewar sa
Yan sanda a Kano na bincike kan mutuwar jami’in kwastam da ake zargin ya kashe kansa
Ana dai ganin samamen da jami’an hukumar ta EFCC sun kai kasuwar ta Wapa yana da nasaba da yadda a yan Kwanakin nan Dala ke cigaba da hauhawa.
Kuma har lokacin hada wannan rahotan jami’an hukumar ta EFCC suna cikin kasuwar ta Wapa.