Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Magana da yawun gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ba da tallafin dogaro da kai ga wasu mata guda 100 da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a Kano.
” Mun ba da wannan tallafin ne domin cika kudirin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na ganin ya inganta rayuwar matan jihar kano”.
Da yake mika tallafin a safiyar yau asabar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sha alwashi cigaba da bata irin wannan tallafin dogaro da kai ga mata da matasa don inganta rayuwar su.
Wani Yaron Ya Sayar Da Ƙodarsa Ya Sayi Wayar Hannu
” Mun zabo ku ne daga mazabun dake karamar hukumar Dawakin Tofa, kuma zamu cigaba da zabo wasu matan domin su ma su amfana”.
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da tallafin ta hanyar da ta gabata, ” ina bukatar don Allah ku yi amfani da tallafin ku kara jarin sana’o’in ku, wanda kuma ba su da Sana’a su fara Sana’ar don ku dogara da kanku.
Abubuwan da ya kamata yan Arewa su yi don amfana da mulkin Tinubu – Kwankwaso
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun godewa mai magana da yawun gwamnan Kano bisa tallafin dogaro da kai da ya basu .
Kimanin mata 100 ne yan asalin karamar hukumar Dawakin Tofa suka amfana da tallafin Naira dubu 10 kowannensu daga mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa.