Daga Abubakar Lawan Bichi
Karamar hukumar Bichi ta rabauta da buhunan shinkafa 2770 tallafi daga gwamantin jihar Kano karkashin jagoranci gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ta samar domin rage radadin ga Jama’a.
Shugaban riko na Karamar hukumar ta Bichi Alh Ahmad Kado Bichi ya karbi Shinkafa tare da saura yan Kwamiti rabon Shinkafar.
Hasashen yanayin da zai kasance yau Juma’a a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Alh Ahmad Kado Bichi yace za’a raba Shinkafa zuwa akwatuna inda mutane Ashirin zasu amfana ako wacce akwa tu.
Ya kuma godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa samar da shinkafa da yayi ga jama’a Karamar hukumar ta Bichi domin rage radadin ga jama’a.
Yanzu-yanzu: An Bayyana Wanda ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasar Chadi
Taro Karba shinkafa ya sami halartar Babban Limamin Masarautar Bichi Sheik Lawan Abubakar ds Babban baturen Yan sanda na Bichi SP Murtala Muhammad Fagam tare da sauran Shuwagabanni hukumomin Tsaro baki daya.