Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau juma’a 10-05-2024 dai-dai da 2 Dhul-Qada 1445 A.H , idan Allah ya so za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 42 bisa ma’aunin zafi.
Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.
Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 40 zuwa 42 bisa ma’aunin zafi.
Kungiyar ASUU ta yiwa gwamnatin Kano barazanar shiga yajin aiki a Jami’ar Maitama Sule
Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.
Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.
Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 37 bisa ma’aunin zafi.
Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 36 bisa ma’aunin zafi
Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 44 bisa ma’aunin zafi.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya Sauke Shugaban Hukumar Haraji Tare da Nada Sabo
Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 43 bisa ma’aunin zafi .
Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 44 bisa ma’aunin zafi.
Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance