Daga Hafsat Lawan Sheka
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Dr. Zaid Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar tara kudaden haraji ta jihar Kano (KIRS).
Gwamnan ya kuma amince da nadin Kassim Ibrahim a matsayin babban darakta na hukumar tara kudaden harajin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce sabon tsarin gudanarwar zai fara aiki nan bada dadewa ba .
Karin Haske Kan Wadanda Sabon Harajin Tura Kuɗi da CBN Suka Fito Da Shi Ya Shafa
Sanarwar ta ce tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Kano Alh. Sani Abdulkadir Dambo ya koma aiki a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari.