Hasashen yanayin da zai kasance Yau Litinin a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau Litinin 06-05-2024 za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 42 bisa ma’aunin zafi.

Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.

Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 40 zuwa 41 zuwa 42 bisa ma’aunin zafi.

Iftila’i: Gobara ta Tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kano

Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.

Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.

Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 36 bisa ma’aunin zafi.

Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 36 bisa ma’aunin zafi.

Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana a gobe Juma’a zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.

Zargin Kisan Kai: Rundunar Sojin Sama ta ba da umarnin bincikar yadda Wasu Sojoji suka kashe wani matashi da duka a Kano

Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 42 bisa ma’aunin zafi .

Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.

Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...