Zargin Kisan Kai: Rundunar Sojin Sama ta ba da umarnin bincikar yadda Wasu Sojoji suka kashe wani matashi da duka a Kano

Date:

Daga Halimatu Musa

 

Al’ummar unguwar Gwagwarwa dake karamar hukumar Nasarawa suna zargin wasu jami’in rundunar Sojin Sama dake Kano da hallaka wani dan unguwar mai suna Yusuf Shu’aibu ba tare da wani daliliba.

A zantawarsa da Jaridar Kadaura24 Mahaifin yaron mai suna Shu’aibu Bala ya bayyana cewa dan nasa ya dawo gida bayan jami’an Sojin dake aiki a asibitin sojojin sama sun yi masa dukan kawo wuka wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar sa har lahira .

Ya ce Dan nas Yusuf ma’aikaci ne a asibitin sojojin sama na kano wanda aka fi sani da suna (465 NAF Hospital), Inda yake yi musu aiki a matsayin mai share-share da goge-goge wato Cleaner.

Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Harbin Da Aka Yiwa Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin jihar

” Bayan ya tashi daga aiki ranar alhamis sai wani cikin ogannisu yace masa ya yi masa wani aikin, shi kuma ya ce Oga Aminu na tashi daga aiki kuma yunwa nake ji, idan zaka siyamin Abinchi sai na tsaya na yi maka aikin ba matsala” inji mahaifin mamacin

” Wai fadin waccan Magana ne yasa shi Oga Aminun ya kirawo wani Soja ya bashi umarnin ya dake shi ( Yusuf) haka ya same shi yayi ta dukansa kamar jaki, wanda kuma Sanadiyar dukan ne Allah ya karɓi rayuwar dana Yusuf” kamar yadda Yusuf ya shaidawa Kunnensa

Yace bayan sun gama dukansa sai ya taho gida jikinsa duk jini sai abokansa suke tambayar sa me ya faru, sai ya basu labari kuma da ya shiga gidan ma sai ya fadawa Kansa da kuma Matar kaninsa babansa , Sanna ya shiga daki ya Kwanta kuma anan Allah ya yi masa cikawa.

Mahaifin yaron yace shi yanzu abun da yake bukata shi ne a yiwa dansa Adalci a hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a wannan lamari domin ya zama izina ga sauran sojoji , domin yace wannan ba shi ba ne Karon farko da irin hakan ta faru don haka idan ba’a dauki Mataki ba to lallai zasu shiga da yiwa al’umma kisan gilla tare da wani daliliba.

Hasashen yanayin yau Lahadi a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

” Ina kira ga dukkanin wasu shugabanni dake karamar hukumar Nasarawa da jihar Kano baki daya musamman gwamnan jihar Kano da masarautar Kano da su taimaka su tabbatar an yi mana Adalci ta hanyar hukunta wadanda suka kashe min da” a cewar Mahaifin yaron da aka kashe

Kadaura24 da yake zantawa da manema labarai, Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya ce Abubakar ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar lamarin tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

Ya ce, “Ina sane da cewa marigayin, Yusuf Shuaibu, ma’aikacin wucin gadi ne a asibitin NAF na Kano 465. Ina kuma sane da cewa, kwanaki 2 da suka gabata, marigayin da wasu sojan sama sun samu sabani wanda ya haifar da damuwa kan rashin biyayya da kuma kin bin wasu umarni da marigayin ya yi.

“Ina kuma sane da cewa bayan rikicin na su, an sasanta lamarin cikin ruwan sanyi, sannan marigayin ya koma gida ba tare da wata alamar rashin lafiya ba, sai dai mun sami labarin washe gari da ya rasu”.

Harbin Bindiga: Wani Dan Jarida ya Tsallake Rijiya da Baya a Gidan Gwamnatin Kano

“Hakika, an sanar da shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Hasan Abubakar labarin rashin imanin da aka yiwa Yusuf Shuaibu, kuma ya nuna damuwarsa. Sai dai ya umarci kwamandojin Asibitin da rundunar sojin sama dake Kano da su mika ta’aziyyarsa da na daukacin Ma’aikatan rundunar ga iyayen mamacin.

“Har ila yau, shugaban rundunar Sojin Sama na Nigeria ya ba da umarnin gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya kai ga mutuwar Yusuf. Don haka ina so in tabbatar muku da cewa ba za a bar wata gaba ha har sai mun bankado abin da ya kai ga mutuwar Yusuf Shu’aibu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...