Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce a halin yanzu tana gudanar da bincike kan lamarin wani harsashi da ya taba wani dan jarida mai aiki a gidan gwamnatin Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho a Kano ranar Asabar, inda ya ce rundunar na kan bincike kan lamarin .
Harbin Bindiga: Wani Dan Jarida ya Tsallake Rijiya da Baya a Gidan Gwamnatin Kano
Ya ce duk shugabannin hukumomin tsaro da ke sanya ido kan harkokin tsaro a gidan sun tsaya kai da fata akan lamarin, wanda hakan yasa aka bincika makaman jami’an tsaro da ke bakin aiki a lokacin da lamarin ya faru, kuma duk an tabbatar alburusansu suna nan babu gibi.
Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Harbin Da Aka Yiwa Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin jihar
Ya bayyana cewa harsashin da akai harbin da shi, daga wajen gidan gwamnatin jihar kano aka harbo shi kuma suna bincke don gano daga inda aka harbo shi.