Hasashen yanayin yau Lahadi a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau Lahadi 05-05-2024 idan Allah ya yarda za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.

Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.

Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 40 zuwa 41 zuwa 43 bisa ma’aunin zafi.

Rundunar Yan Sandan ta Bayyana Matsayarta Kan Harsashin Da ya Taba Dan Jarida a Gidan Gwamnatin Kano

Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.

Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.

Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 37 bisa ma’aunin zafi.

Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Harbin Da Aka Yiwa Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin jihar

Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 36 bisa ma’aunin zafi

Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana a gobe Juma’a zai kai 44 bisa ma’aunin zafi.

Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 44 bisa ma’aunin zafi .

Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 44 bisa ma’aunin zafi.

Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...