Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugabar kungiyar mata yan jaridu ta kasa reshen jihar kano Hajiya Hafsat Sani Usman, ta tabbatar da goyon bayanta ga matakan da kungiyoyin NUJ da RATTAWU suka dauka kan tambarwarsu da shugaban gidan talabijin na ARTV Alhaji Mustapha Indabawa.
” Da ni aka zauna aka tattauna har aka fitar da matsayar da aka fitar, kuma Ina tare da su akan wannan dambarwar kuma NAWOJ ba za ta taba kwayewa NUJ da RATTAWU baya ba muna tare da su dari bisa dari”.
Kadaura24 ta rawaito Hafsat Sani Usman ta bayyana hakan ne lokacin da take musanta batun da shugaban gidan talabijin na ARTV yayi na cewa basa tare da gwagwarmayar da sauran kungiyoyin gidan talabijin din ke yi .
Zargin Almundahana: Gwamnatin Kano Ta Fara Bincikar Shugaban Gidan Talabijin Na ARTV
” A matsayina ta shugabar kungiyar NAWOJ ta jihar Kano ba mu yi magana da MD na ARTV ba, ballantana na fada masa cewa bama tare da sauran kungiyoyin ARTV ba, hasali ma ni bana kano kuma bani da Lambar wayarsa balle mu yi Magana da shi”. Inji Shugabar NAWOJ
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa kungiyoyin NUJ da RATTAWU da NAWOJ sun koma da yadda shugaban gidan talabijin din yake tafiyar da harkokin tashar, tare kuma da zarginsa da kokarin yi musu barazanar chanza su daga gidan talabijin din.
Hukumar NEMA ta Bayyana Adadin Wadanda Suka Rasu a Hatsarin Ginin da Afkawa wasu a Kano
Sai dai a wata tattaunawa da yayin da majiyar kadaura24 MD na ARTV ya ce kungiyar NAWOJ ta fada masa cewa bata tare da abubunwan da NUJ da RATTAWU suke yi ga kokawa da yadda yake tafiyar da harkokin tashar.
” Ina kara jaddada cewa duk matakan da NUJ da RATTAWU suka dauka mu NAWOJ muna tare da su dari bisa dari ba gudu ba ja da baya”. A cewar Hafsat Sani Usman