An janye ƴan sandan da ke samar da tsaro ga hukumar da Muhuyi ke jagoranta

Date:

Babban sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya janye ƴan sanda kimanin 40 da ke samar wa hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano tsaro.

Matakin ya zo ne bayan binciken badaƙalar kuɗi da hukumar, ƙarƙashin jagorancin Muhuyi Magaji Rimin Gado take yi kan shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Sanarwa ta Musamman Daga Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Kano

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa babban sufeton ƴan sandan ya bayar da umarnin janye ƴan sandan ga kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel.

Wata majiya da jaridar ta ruwaito ta ce wasu cikin ƴan sandan suna taimaka wa hukumar ta yaƙi da rashawa a Kano a binciken da take yi tare da samar da tsaro ga hedikwatar hukumar da sauran dukiyoyin da ake bincike a kansu.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...