Gwamna Abba Kabir Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwar Dr. Faizu Baffa Yola

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar Dakta Faizu Baffa Yola wanda ya rasu a yau (Alhamis) sakamakon rashin lafiya da ya yi yana da shekaru 74 a duniya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya Kasance cikin jimami bisa rasuwar saboda da gudunmawar da Marigayi Dokta Faizu Baffa Yola ya bayar wajen ci gaban harkokin kiwon lafiya a jihar kano baki daya.

Tsakananin zafi: Hukumomi a Kano sun ba da shawarwarin kare kai ga al’umma

“Babu shakka an yi Babban rashin da baza a taba iya maye gurbin sa Saboda Dakta Faizu ya taimaki al’umma daban-daban a fannin da ya kware kasancewarsa kwararren Likita .

“A madadin gwamnati da na al’ummar jihar nan, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa da al’ummar jihar, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya sa Aljannar Firdausi ta kasance makomarsa.” Ya yi addu’a ga Gwamnan.

Mun dauki matakan shawo kan matsalar mai a Nigeria – NNPC

Marigayi Dokta Faizu Baffa Yola ya kasance gogaggen Likita wanda ya ke aikin sirri kafin a nada shi kwamishinan lafiya a jihar Kano a zamanin marigayi Kanar Muhammad Abdullahi Wase.

An kuma nada shi Kwamishinan Albarkatun Ruwa a Kano a zamanin Marigayi Birgediya Janar Dominic Obukadata Oneya.

Ya shiga siyasa kuma a lokaci daya ya tsaya takarar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin rusasshiyar jam’iyyar NRC.

Dr. Fa’izu Baffa shi ne likita na 5 dan asalin jihar Kano da ya yi aiki a Kano kuma ya ci gaba da aikin jinya da tiyata har ya rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...