Daga Halima Musa Sabaru
Wani abin takaici ya faru a Kano yayin da aka sami gawar wani jariri ya nutse a cikin rijiya da ke Ruguzau a karamar hukumar Takai a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bayyana Dalilanta na Rufe Bankin UBA A Jihar
Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 02:14 na rana daga wani Sabo Ladan cewa an tsinci gawar wani jariri a cikin wata rijiya a garin ruguzau.
“Nan take muka aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 02:18 na rana. Da isa su wajen sai suka sami jariri a cikin rijiyar,” inji shi.
A cewarsa, an fito da jaririn daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da cewa ya mutu.