Ganduje ya kaddamar da hanyar da aka sanyawa sunansa a Gombe

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, a ranar Larabar nan ya kaddamar da wata hanya da gwamnatin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta gina wadda aka sanyawa sunan sa a Gombe.

Titin mai tsawon kilomita 1.6 ya taso daga GRA zuwa Gombe Southern By-pass, wanda ya hada garuruwan Nayi-Nawa, Kuwait, Bagadaza, Hammadu kafi, da Wuro Biriji a cikin karamar hukumar Akko, a cikin babban birnin Gombe.

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan jihar Gombe Isma’il Uba Misilli ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Gombe.

Gwamnan Kano da Takwarorinsa Suna Halartar Taron Zaman Lafiya a America

A yayin kaddamar da aikin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa yadda ya kawo sauyi a jihar Gombe, inda ya bayyana irin gagarumin ci gaban da jihar ta samu a karkashin jagorancinsa wanda ya ce ya dace da muhimman abubuwan da ya kamata a gudanar a jihar, Inda yace aiyukan da yake suna cikin manufofin da aka kafa APC akan su.

“A yau muna garin Gombe bisa gayyatar dan uwana mai girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON domin gudanar da harkokin siyasa dangane da zaben kananan hukumomi da ke tafe, abin farin ciki na, gwamna ya zabe ni ya karrama ni ta hanyar sanya suna na a muhimmiyar hanya da ya gina”, in ji Shugaban APC.

 

“Shugaba Tinubu da jagororin jam’iyyar mu suna matukar alfahari da irin nasarorin da Gwamna Inuwa Yahaya ya samu, ya nuna misali da kawo sauyi mai kyau a jihar Gombe, muna sane da dimbin ayyukan more rayuwa da ayyukan jin dadin da walwalar jama’ar jihar Gombe, ,” inji Ganduje.

Iftila’i: An Sami Gawar Wani Jariri Cikin Rijiya a Kano

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya ci gaba da cewa, sabuwar hanyar da aka kaddamar za ta magance wahalhalun da masu bin hanyar ke fuskanta, inda ya jaddada yuwuwar hanyar da za ta bunkasa rayuwa da bunkasa harkokin kasuwanci a yankunan.

Sai dai ya ja hankalin al’ummar jihar Gombe baki daya da su ci gaba da marawa gwamnatin Inuwa Yahaya baya don ganin an samar da ingantaccen shugabanci ta hanyar ayyuka da tsare-tsare da nufin inganta rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...