Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf Kabir ya isa kasar Amurka domin wani gagarumin taron tattaunawa da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sunusi Bature ya fitar a ranar Laraba.
Iftila’i: An Sami Gawar Wani Jariri Cikin Rijiya a Kano
Taron wanda za a shafe kwanaki uku ana gudanarwa, ya samu halartar gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Neja, Sokoto, Kebbi, Jigawa, da Filato.
Bature ya ce, taron ana sa ran zai kawo hanyoyin da za a bi don magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya.